A karon farko a tarihin Kenya an fara kirga dabbobin dawa dake fadin kasar.
Hukumar Kula da Dabbobin Dawa ta Kenya (KWS) ta bayyana cewa, manufar kidayar da aka fara daga Lambun Shakatawa na Tsaunukan Shimba ita ce a san yawansu da kuma inda suke.
KWS ta bayyana cewa, za yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen kirga dabbobin na dawa.
Ministan Harkokin Yawon Bude Ido na Kenya Najib Balala ya bayyana cewa, a yayin kidayar zasu mayar da hankali don gano dabbobin da suke cikin hatsari sannan a hana farautarsu da ake yi ba bisa ka'ida ba.
A Kenya akwai filayen shakatawa na kasa da dama kuma suna dauke da daruruwan nau'ikan dabbobin dawa.