An fara binne gawar mutum 2,000 a Gabashin Jamhuriyar Congo

An fara binne gawar mutum 2,000 a Gabashin Jamhuriyar Congo

Ministan sadarwa na Congo, Patrick Muyaya ya ce, an dan samu kwanciyar hankali a yankin, bayan da ‘yan tawayen suka sanar da tsagaita wuta domin bayar da damar kai agajin jin kai.

Sai dai wasu mazauna yankin sun ce, sun jiyo amon harbe-harbe, abin da ake ganin ya haifar da tururuwar mutane a asibitoci, inda a wasu wuraren ma an ga yadda mutane ke kwance akan hanyoyi.

Muyaya, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, yawan mutanen da aka tabbatar za a binne gawarsu, ya nuna irin aikin ta’addancin da ‘yan tawayen suka yi.

Goma da ke gabashin Congo na dauke da arzikin albarkatun kasa irin su zinare da Coltan da kuma tama.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa, mutum 900 aka kashe, inda kusan 3,000 suka samu munanan raunuka, sakamakon hare-haren ‘yan tawayen.

Sama da mutum dubu 700 ne suka rasa muhallancu a Goma a watan jiya kadai, a cewar rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar na zargin ‘yan tawayen na M23 da dakarun Congo, da take hakkin dan adam, da suka hada da kisa da kuma fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)