An dakko Turkawan da suka mutu da jikkata a Somaliya zuwa Turkiyya

An dakko Turkawan da suka mutu da jikkata a Somaliya zuwa Turkiyya

Jirgin saman Turkiyya ta taso daga Mogadishu zuwa Istanbul dauke da gawarwakin Turkawa 2, Selami Aydogdu da Erdinc Genc da suka rasa rayukansu, da kuma wasu karin leburori 4 da suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai a Somaliya.

Daya daga cikin wadanda suka jikkata Omer Aydogdu da aka dakko a jirgin saman da ya taso daga Mogadishu-Djibouti zuwa Istanbul, ya shaidawa 'yan jaridu cewa, an kai musu harin a lokacin da suke zuba kwalta a kan hanyar da su ke samarwa.

Aydogdu ya shaida cewar, bayan fashewar bam din dukkan su sun fadi kasa.

Ya ce "Ni da dana muna aiki a wajen. Dana ya rasu. Ina matukar bakin ciki."

Aydogdu ya ce, su 6 ne suka tafi Somaliya don yin aiki daga yankin Corum na Turkiyya.

Mutum na 2 da ya jikkata mai suna Yavuz Ercan ya shaida cewar, abun bakin ciki ne yadda aka kai musu harin, amma ya tsira da ransa inda ya ce "Mun rasa 'yan uwanmu. Ina ma dai ba a kai harin ba. Amma babu yadda za a yi."

Imdat Uzuncakose da ya samu rauni ma ya bayyana matukar bakin cikinsa game da kai harin.

Haka zalika mutum na 4 da ya samu rauni a kafarsa, Sakir Cetinkaya ya fadi cewa, an kwashe su nan da nan zuwa asibiti bayan kai harin.

A ranar 2 ga watan Janairu ne aka kai harin bam kan wani kamfanin gina yanyoyi na Turkiyya da ke aiki a Mogadishu Babban Birnin Somaliya inda aka kashe Turkawa 2 da jikkata wasu 4.


News Source:   ()