Sakamakon annobar Corona (Covid-19) an dakatar da Tattaunawar Sulhun Siyasar Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar gudanarwa a Swizalan.
Bayanan da kamfanin dillancin na Anadolu ya samu daga mahalarta Taron na cewa, sakamakon samun mutane 2 da ke halartar taron dauke da Covid-19 ya sanya an dakatar da gudanar da shi.
A garin Nyon na Sizalan ne aka fara gudanar da taron da ke tattaunawa kan batun zabuka da za a gudanar a ranar 24 ga Disamba a Libiya.
Sakamakon yadda aka bukaci dukkan mahalarta taron da su yi gwajin PCR ne ya sanya ba a iya ci gaba ba a safiyar Larabar nan.