An dakatar da Mali daga ECOWAS

Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dakatar da Mali daga zama mamba sakamakon rikicin siyasar da ake yi a kasar.

Shugabannin kasashe mambobin ECOWAS sun gudanar da taron gaggawa a sirrance a Accra Babban Birnin Gana.

Ministar Harkokin Wajen Gana Shirley Ayorkor Botchwey ta yiwa manema labarai bayani bayan kammala taron inda ta sanar da an dakatar da Mali daga zama mambar ECOWAS.

Botchwey ta kara da cewa, wannan mataki ya yi daidai da tafarki da tsarin demokradiyya.

Ministar ta yi nuni da cewa, ECOWAS ba ta amince da abubuwan siyasa da ke afkuwa a Mali ba.

Ta ce, "Dukkanmu muna tunanin za a koma aiki da kundin tsarin mulki kuma a mikawa farar hula mulki nan da karshen shekara mai zuwa. Amma abun takaici sai ga shi wani abu daban na faruwa a kasar."

Ta ce, duk da dakatar da Mali daga kungiyar, shugabannin siyasa da na soji na kasar za su ci gaba da aiki da ECOWAS don ganin an mayar da mulki ga farar hula.

A ranar 18 ga Agustan 2020 ne aka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a Mali inda aka kafa gwamnatin wucin gadi.

Bayan yin kwaskwarima a majalisar ministoci a Mali ne ya sanya sojojin kasar suka kama Shugaban gwamnatin wucin gadi Bah N'Daw da Firaminista Mouctar Ouane tare da sauran manyan jami'an gwamnatin.

A ranar 27 ga Mayu aka saki shugabannin bayan sun yi murabus. Daga baya kuma kotun koli ta Mali ta bayyana Assimi Goita da ya goranci juyin mulkin kasar a matsayin Shugaban riko.


News Source:   ()