Sanarwar da ma’aikatar kula da ƴan asalin Mali mazauna ketare ta fitar, ta ce jirgin ruwan ya kife ne lokacin da ya ke ɗauke da mutane kusan 80, kuma 11 cikinsu ne kaɗai suka tsira da ransu.
Tuni mahukuntan ƙasar suka kafa kwamitin da zai yi bincike tare da tattara bayanan musabbabi faruwar hatsarin.
An samu ƙaruwar ƴan cirani da ke hanƙoran kwarara daga nahiyar afrika zuwa yankin turai a shekarar 2024.
Rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin Saleh ciki har da Mali, baya ga rashin aikinyi da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga yankunan da suka dogara da noma, na daga cikin dalilan da ke sanya jama’a ficewa daga ƙasar.
Aƙalla ƴan ci rani dubu 5 ne suka mutu a cikin teku lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasar Spain a watanni 5 na farkon shekarar 2024, adadin da ba’a taɓa gani ba cikin shekaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI