Gwamnatin tarayya da shugabannin jihohi a Somaliya sun amince da gudanar da zabe cikin kwanaki 60 don magance rikicin zabe da ya kai kasar gab da yakin basasa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron ba da shawara kan zaben kasa da aka gudanar a babban birnin kasar, Mogadishu, Firaministan Somaliya Mohammed Hussein Roble ya bayyana cewa an kammala tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin jihohi game da rikicin zaben ba tare da wata matsala ba.
Roble ya bayyana yarjejeniyar kan tsarin zaben a matsayin wani lokaci a tarihi mai muhimmanci inda ya lura da cewa shugabannin sun amince a gudanar da zabe cikin kwanaki 60.
An rawaito cewa gwamnatin tarayya da shugabannin jihohi a Somaliya sun cimma wata yarjejeniya a ranar Talata don warware rikicin zaben da ya kai kasar gab da yakin basasa.