An cika shekaru 80 da kisan gillan Thioraye a Senegal

An cika shekaru 80 da kisan gillan Thioraye a Senegal

Rana 1 ga watan Disamba 1944  sojojin Faransa suka budewa takwarorinsu da suka tare a sansanin Thiaroye dake Senegal  wuta.

Shekaru 80 bayan afkuwar lamarin har yanzu ana tantama gameda ainahin abunda ya faru da dakarun bakaken fata yayin da ‘yan uwa wadanda suka bace keta neman Faransa ta daukin alhakin abunda ya faru a hukumance.

A cewar wasu masana da suka dukufa tsawan shekaru wajan gano hakikanin abunda ya faru, tarihin Thiaroye an ginasa bisa karai-karayi guda uku.

Karya  farko bincken ya nuna an biya wadanda suka mutu dukanin hakokin su,yayin da kariya ta biyu kuwa aka kasa bayyana gaskiya adadin wadanda aka kashe ba, ta ukun da tafi kowace muni shi ne sabanin abunda kowa ya yi tsammani ba’a binne dakarun bakaken fata  a makabarta soji ba.

A rana 28 ga watan Disamba da ya gabata, Shugaban na Senegal Bassirou Diomaye Faye ya fada yayin wata hira da ‘yan Jarida cewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da aikata gisan killan a Thioraye.

Sai dai ‘yan majalisa dokoki a kasar sun bukaci kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike akan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)