An ci zarafin mata 260 ta hanyar fyaɗe a gidan yarin Congo- MDD

An ci zarafin mata 260 ta hanyar fyaɗe a gidan yarin Congo- MDD

Wani rahoton Majalisar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya ce yayin yamutsun ɓalle gidan yarin na Makala aƙalla mata 268 cikin 348 da ke gidan yarin sun fuskanci cin zarafi galibinsu ta hanyar fyaɗe ciki kuwa har da yara mata 17 da shekarunsu na haihuwa bai kai 19 ba.

Rahoton ya ce akalla mutane 129 suka mutu a yamutsin bayan da jami’an tsaro suka buɗe wuta kan fursunonin da ke ƙoƙarin tserewa daga gidan yarin na birnin Kinshasa mai ɗaukar mutane dubu 1 da 500 amma kuma aka danƙare fursunonin da yawansu ya haura dubu 15.

Tun gabanin rahoton Majalisar ɗinkin duniyar, mahukuntan Congo sun bayyana cewa tabbas mata da dama sun fuskanci cin zarafi ta hanyar fyaɗe amma basu bayar da cikakkun alƙaluman matan da abin ya shafa ba.

Majalisar ɗinkin duniya ta koka da cewa duk da yadda mahukuntan na Congo ke da masnaiya kan cin zarafin matan, amma an gaza basu kulawar da ta dace lura da cewa suna buƙatar garzayawa da su ga likita cikin ƙasa da sa’o’i 72.

Wata mata da Reuters ta zanta da ita ta ce Gomman maza ne suka yi mata fyade kuma haka ne ya faru ga kusan dukkanin matan da suka fuskanci wannan cin zarafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)