An bukaci 'yan adawar Masar da su ci gaba da zanga-zanga

An bukaci 'yan adawar Masar da su ci gaba da zanga-zanga

Wani dan adawar Masar da ke rayuwa a Spaniya, Muhammed Ali ya yi kira da a ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar mai mulki.

A jawabin da Ali ya yi a wata tashar talabijin ya yi kira ga 'yan adawar da ke zaune a Masar da su ci gaba da gudanar da zanga-zanga a kowacce rana.

Ali ya yi nuni da zanga-zangar da aka gudanar kwanaki 2 da suka gabata a garuruwan Giza, Asvan da Iskandariyya, inda ya yi kira da a karya shingayen jami'an tsaro.

A ranar 20 ga watan Satumban 2019 da ta gabata ne Ali Muhammed ya yi kira da a fita zanga-zangar adawa da Shugaban masar Abdulfatah Al-Sisi, wanda a yanzu ya sake yin kiran bayan shekara guda.

Mutane da dama sun amsa kiran tare da fita zanga-zanga, an kama da yawa daga cikinsu amma an saki mafi yawansu daga baya.

Gamayyar Majalisar Adawa da Kifar da Zababben Shugaban Kasar Masar na farko Muhammad Mursi, sun bayyana suna goyon bayan zanga-zangar adawa da Abdulfatah Al-Sisi da al'uma ke yi a Masar din.


News Source:   ()