jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi gargaɗin cewa ja-in-ja da ake ci gaba da yi a Sudan ya kai ta daf da tsinkewa, kuma za a samu ƙarin dubban mace-mace da za a iya kauce wa a cikin watanni masu zuwa sakamakon yunwa, cutuka, ambaliya da kuma ta’azzarar rikici idan babu wani mataki daga ƙasashen duniya.
Rundunar RSF, wadda ta karɓe iko da wasu sassan ƙasar ta aike da wakilai taron, amma tattaunawa ta kai tsaye ba za ta yiwu ba idan babu wakilcin sojin Sudan, kamar yadda jakadan Amurka na musamman a Majalisar Ɗinkin Duniya,Tom Perriello, wanda ya jagoranci yunƙurin shiga tsakanin ya bayyana.
A maimakon haka,halarta tattaunawar da suka haɗa da Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Afrika da ƙungiyar ƙasashen Gabashin Afrika da ƙwararru za su yi nazari a kan hanyoyin da za a bi wajen dakatar da hare -hare da lalubo yadda za a isar da kayayyakin agaji.
Rundunar sojin Sudan ta ce ƙin halartar taron da ta yi ,ya samo asali ne daga rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tun da farko ta cewa RSF za ta janye dakarunta daaga yankunan farar hula, amma masu shiga tsakani sun zargi dukkan ɓangarori da rashin mutunta matsaya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI