A watanni 7 da suka gabata a Najeriya, an biya kudi kimanin dalar Amurka miliyan 2,4 don fansar daliban da aka yi garkuwa da su.
Labaran da jaridar Punch ta fitar na cewa, wani rahoto kan tsaron kasa da aka fitar ya bayyana Najeriya na tsaka da fuskantar matsalolin tsaro.
Rahoton ya bayyana an biya kudi har dala miliyan 2,4 don karbar daliban da aka yi garkuwa da su a yayin hare-haren 'yan bindiga sau 5 a arewa maso yammacin Najeriya a tsakanin watan Nuwaban 2020 da Mayun 2021.
Amma gwamnatin Najeriya ta ce, ba a biya kudin fansa ba don a saki daliban.