Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Burkina Faso

Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Burkina Faso

Hari na farko an kai shi ne a ranar asabar 5 ga wannan wata kan ayarin jami’an tsaro da ke sintiri kusa da garin Bogande na lardin Gnagna a arewa maso gabashin kasar, inda aka ruwaito cewa sojoji 17 sun rasa rayukansu.

Sai hari na biyu a ranar lahadi lokacin da mutane ke cin kasuwa a wani gari mai suna Manni da ke da tazarar kilomita 200 daga birnin Ouagadougou fadar gwamnatin ƙasar,  kuma hotunan bidiyo da aka riƙa yaɗawa sun nuna ɗimbin shaguna na ci da wuta, yayin da wasu hotunan ke nuna mutane da dama kwance a asibitin garin sakamakon raunukan da suka samu.

An kai harin ne washe-garin jawabin da shugaban ƙasar Keftin Ibrahim Traore ya gabatar wa al’umma, inda yake jaddada cewa za su ci gaba da ɗaukar matakai domin murƙushe ayyukan ta’addanci a duk fadin kasar.

Har zuwa wannan lokaci dai ba wata ƙungiya da ta fito fili ta ɗauki nauyin kai waɗannan hare-hare, to sai dai bisa ga al’ada waɗannan yankuna ne da ƙungiyoyin masu da’awar jihadi suka saba kashe jami’an tsaro da kuma fararen hula a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)