Ƴan bindiga sun kashe fararen hula sama da 35 a Gabashin Congo

Ƴan bindiga sun kashe fararen hula sama da 35 a Gabashin Congo

Basaraken ƙauyen Djugu, Jean Vianney ya ce ƴan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 8 na daren jiya Litinin, inda suka kashe mutane tare kuma da ƙona gidaje.

Ya ce izuwa safiyar Talatar nan, sun gano gawarwaki sama da 35, bayaga waɗanda suka samu raunuka da kuma asarar dukiyar da aka tabka.

Shugaban wata ƙungiyar farar hula a yankin Jules Tsuba, ya ce izuwa safiyar yau Talata, sun gano gawarwakin da suka kai 49, kuma har yanzu ana ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.

Ita dai ƙungiyar CODECO na daga cikin ƴan bindigar da ke kai hare-hare a Gabashin Congo, inda a shekarun baya Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargeta da kai hare-hare kan makiyaya ƴan kabilar Hema, wanda ka iya sanya a tuhumi ƙungiyar da aika laifukan yaƙi da keta hakkin dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)