A rahoton mako-mako da ma’aikatar tsaron ƙasar ta saba fitarwa, gwamnatin ta ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin rana asabar daidai lokacin da kasuwar kauyen ke tsaka da ci, abunda ya sa aka samu asarar rayukan fararen hula da dama.
Rahoton ya ƙara da cewa ko a ranar Juma’a da ta gabata sai da dakarun ƙasar biyu suka mutu bayan da ayirin motocinsu ya taka wani abun fashewa da aka dana a kauyen Tiyawa duk dai a Jihar ta Tillabery.
Da ya ke jagorantar zana’izar waɗanda suka mutu a harin, gwamnan Jihar Tillabery Kanal Maina Bukar ya jajintawa iyalansu da sunan gwamnati, tareda fatan samun lafiya ga waɗanda sukaji rauni.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da dakarun ƙasar ke ƙara kaimi wajan fatattakar ƴan bindiga da ke addabar jama’a a wanan yankin da yaraba iyaka da ƙasashen Mali da Burkina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI