Ofishin Mai Gabatar da Kara na Rundunar Sojin Libiya ya bayar da umarni da a kama Saifulislam, dan tsohon hambararren Shugaban Kasar Muhammad Ghaddafi sakamakon zargin sa da aikata kisan kai da amfani da sojojin haya.
Kafafan yada labarai na Libiya sun bayyana cewa, a wani umarni da aka aikawa sojoji da 'yan sandan kasar a ranar 5 ga Agusta, an bayyana da a kamo Saifulislam tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin sa da aikata kisan kai da amfani da sojojin haya.
A matakin an baiwa dukkan cibiyoyin sojna kasar da su bazama neman Saifulislam tare da kamo shi.
An bayyana cewa, wannan mataki ya zo ne a wani bangare na binciken da ake yi game da Farmakan Onur inda sojojin haya na Rasha (Wagner) suka aikata kisan kai ga jama'a.
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa na neman Saifulislam bisa zargin sa da laifukan keta hakkokin dan adam.
Tsohuwar Mai Gabatar da Kata ta Kotun Fatou Bensouda a ranar 17 ga Mayu ta yi kira ga Saifulislam da ya mika wuya ko kuma mahukuntan Libiya su mika shi.