An bayar da belin jagoran 'yan adawa da wasu mukarabansa a Tanzania

An bayar da belin jagoran 'yan adawa da wasu mukarabansa a Tanzania

Tuni dai jam'iyyar Chadema ta yi zanga-zanga a farkon makon nan don nuna rashin amincewa da matakin "rashin adalci" da aka yi wa wasu 'yan takararta a jajibirin zaben da aka gudanar a garuruwa da kauyukan kasar.

Ana sa ran zaɓen na ranar Laraba ya zama maƙasudin yanayin siyasa kafin zaɓen shugaban ƙasar da aka shirya gudanarwa a watan Oktoban 2025 a ƙasar.

"A wannan dare, an ba da belin shugaban Chadema Freeman Mbowe (...) da kuma sauran shugabannin da aka tsare a ofishin 'yan sanda na Vwawa," in ji jam'iyyar siyasa a safiyar yau Asabar a dandalin sada zumunta na X.

Jagoran yan adawa a kasar Tanzania Chadema, Freeman Mbowe Jagoran yan adawa a kasar Tanzania Chadema, Freeman Mbowe REUTERS - Emmanuel Herman

An kama jagoran yan adawa a ranar Juma'a tare da wasu jami'ai bayan 'yan sanda sun tarwatsa taron "ta amfani da hayaki mai sa hawaye", a cewar jam'iyyar.

Bayan da aka sake shi jagoran 'yan adawar ya yi magana da 'yan jarida, inda ya ce: "An zarge mu da karya jadawalin yakin neman zabe amma ba shi da tushe." Chadema Freeman Mbowe ya kara da cewa "Ina ganin wannan wani shiri ne da gangan don kawo cikas ga yakin neman zaben da muka tsara.

Tanzaniya ta fuskanci tsanantar danniya ta siyasa a cikin 'yan watannin nan. Jam'iyyar Chadema dai na zargin jami'an tsaro da hannu a bacewar wasu mambobinta da kuma kisan Ali Mohamed Kibao, daya daga cikin shugabanninta da aka samu gawarsa a ranar 7 ga watan Satumba. Tuni dai aka kama Chadema Freeman Mbowe na wani dan lokaci a karshen watan Satumba tare da mutane da dama lokacin da 'yan sandan Tanzania suka hana zanga-zangar da jam'iyyarsu ta gudanar a Dar es Salaam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)