
Mai magana da yawun ƴantawayen na ƙungiyar FLA Mohamed Elmaouloud Ramadane, ya ce an kakkaɓo jirgin ne a ranar Talata, lokacin da ya ke sauka a wani bariki da ke Tissalit na arewacin ƙasar.
To sai dai a wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Mali, ta ce dakatunta sun yi nasarar kama wani jirgi maras matuƙi da ƴanta’adda ke amfani da shi a daidai lokacin da yake ƙoƙarin yin leƙen asiri game da ayyukan soji.
Sanarwar ta ce yanzu haka ƙwararru daga rundunar soji ƙasar sun fara aiki a game ƙwaƙwalwar taera wanda ke tattare da bayanan sirin jirgin, domin sanin haƙiƙanin bayanan da ke ƙunshe a cikinsa.
An dai shere kusan shekaru 13 ana fama da rikici a yankin arewacin Mali, inda Azbinawa ƴan aware suka ɗauki makamai domin ɓallewa da kuma samar wa yankin cikakken ƴancin. To sai dai martanin da rundunar sojin Mali ta mayar ya kasance zazzafa, inda a watan Nuwambar 2023 dakarun na gwamnati suka yi nasarar fatatakar ƴantawaye daga babban tungarsu da ke garin Kidal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI