An aiyana Zamfara a matsayin yankin da jiragen sama ba za su yi zirga-zirga ba

An aiyana Zamfara a matsayin yankin da jiragen sama ba za su yi zirga-zirga ba

Gwamnatin Najeriya ta aiyana jihar Zamfara a matsayin yankin da jiragen sama ba za su yi zirga-zirga a cikin sa ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Majalisar Tsaro ta Kasa a Fadar gwamnati sakamakon hare-haren da ake yawan kai wa a jihar Zamfara tare da garkuwa da mutane.

Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan tsaron Kasa Babagana Monguno ya zanta da manema labarai bayan gudanar da taron inda ya ce, Shugaba Buhari ya aiyana Zamfara a matsayin yankin da ba za a dinga zirga-zirgar jiragen sama a cikin sa ba.

Monguno ya kara da cewa, Buhari ya kuma hana aiyukan hakar ma'adanan zinariya a jihar, kuma ya bayar da umarni ga jami'an sojin da aka kai da su samar da tsaro nan da nan.

Monguno ya yi nuni da cewa, jami'an tsaron za su kwato dukkan yankunan da suke hannun 'yan bindiga inda ya ce,

"A lokacin da mu ke kaiwa 'yan bindiga hari ba za mu damu da wai za a kashe fararen hula ba. Ba za mu sake yarda da bata suna ba. gwamnati na da alhakin aiwatar da manufofinta."

A ranar 26 ga Fabrairu 'yan binciga sun yi garkuwa da 'yan mata dalibai 317 a makarantar sakandire ta Jengebe da ke jihar Zamfara, a ranar Talatar nan aka kubutar da 279 daga cikin su.


News Source:   ()