An aiyana zaman makoki na kwanaki 3 a fadin kasar Mali sakamakon harin ta'addancin da aka kai a yankin Gao tare da kashe mutane da dama.
Shugaban Kasar Mali na Wucin Gadi Assimi Goita ya fitar da sanarwa ta shafin Twitter cewa, sun yi bakin ciki da samun labarin kai harin, sun kuma la'ance shi.
Ya ce, dakarun sojin Mali sun fara kai farmakai don nemo maharan tare da kassara su, kuma za su ci gaba da yaki da ta'addanci a kasar sama da koyaushe.
Goita ya ce, sun aiyana zaman makoki na kwanaki na awanni 72 sakamakon mutuwar mutane da dama a harin na ta'addanci.
Wasu 'yan ta'adda da ba a san ko su waye ba ne suka kari kan kauyuka 4 na yankin Ansongo da ke Mali tare da kashewa da jikkata mıutane da dama.