A Jamhuriyar Nijar an aiyana zaman makoki na kwanaki 3 sakamakon harin da aka kai a karshen makon da ya gabata tare da kashe mutane 28.
Kakakin gwamnatin Nijar Zakaria Abdurrahman ya shaida cewar, gwamnati ta aiyana zaman makoki na kwanaki 3 da ya fara daga ranar Talatar nan don tunawa da wadanda aka kashe a harin na ta'addanci.
A daren da ya hada ranakun Asabar da Ladin karshen makon da ya gabata ne 'yan ta'addar Boko Haram suka kai hari a kauyen Toumour da ke yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar.
An kashe mutane 28 tare da lalata gidaje da wuraren sana'a sama da 800 a yayin kai harin.
A ranar 11 ga watan Disamba ma 'yan ta'addar Boko Haram sun kai wa yankin na Diffa hari tare da kashe mutane 2.
Tun shekarar 2015 yankin Diffa da ke da iyaka da arewacin najeriya ya ke fuskantar hare-haren 'yan ta'addar Boko Haram.