Cikin masu ƙima a Afirka a wannan sabuwar shekara harda Aboubakary Siddiki shugaban jam’iyyar CNPS mai adawa a ƙasar Kamaru kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen daƙe tafe cikin wannan shekara.
Zaɓeɓɓen shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahamat da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribado da Idris Elba mawaƙi kuma jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Amurka na daga cikin mutane 100 masu kima a Afirka a wannan shekara.
Ƙungiyar ta ce, Siddiki ya sadaukar da kansa don kawo sauyi da ci gaba a Kamaru, ya mayar da hankali kan hadin kan kasa, adalci na zamantakewa, da ci gaban tattalin arziki, tare da himma don magance matsalolin da kasarsa ke fuskanta.
Za a karrama mutanen yayin wani katsaitaccen biki da za’a gudanar a Afirka ta Kudu a hukumance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI