Amurka ta tura fursuna mafi ɗaɗewa a Guantanamo zuwa gida Tunusiya

Amurka ta tura fursuna mafi ɗaɗewa a Guantanamo zuwa gida Tunusiya

Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa an dawo da Ridah bin Saleh al-Yazidi mai shekaru 59 wanda ke zama mafi daɗewa a gidan yarin sojojin Amurka da ke Cuba zuwa Tunisiya a ranar Litinin din da ta gabata.

Wannan shine karo na hudu a cikin makonni biyu da gwamnatin Biden mai barin gado ta yi a ƙoƙarin rage yawan fursunonin a Guantanamo , wanda ke rike da fursunoni 40 lokacin da Biden ya hau karagar mulki a shekarar 2020.

Jami'an Amurka sun zargi Yazidi da kasancewa mamba a wata ƙungiyar da ake zargi da alaka da al-Qaida, amma ƙungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna musanta wadannan ikirari.

Kungiyoyin kare hakkin sun ce an tsare shi a gidan yarin tun a shekarar 2002, wanda hakan ya sa ya kasance ɗaya daga cikin wadanda suka ɗaɗe a tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)