Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce sun sanya takunkumi kan Janar Mohamed Hamdan Dagalo ne saboda rawar da ya taka wajen cin zarafin al'ummar Sudan a cikin watanni 20 na rikicin.
Ya ce ƴan tawayen RSF da kawancensu na da alhakin kisan maza da mata da ƙananan yara har ma da jarirai", da kuma cin zarafi ta hanyar lalata bisa dalilai na kabilanci.
Blinken ya ce, mayaƙan RSF sun kuma kai hare hare kan fararen hula da ke tserewa tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ke tserewa rikicin.
To sai dai, a martaninta RSF ta zargi Amurka da munafurci, da kuma rashin bin hanyoyin da suka dace wajen magance rikicin
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI