Harin da Amurka ta kai a yau ya ruguza kogon da suke zaune a ciki tare da kashe ‘yan ta’adda da dama ba tare da cutar da fararen hula ba” a wannan kasa da ke yankin kahon Afirka, in Shugaban na Amurka.
Donald Trump bai bayyana sunan jami'in ba ko kuma ya tabbatar da mutuwarsa.
Wannan dai ne karo na farko tun bayan hawan karagar mulkin Donald Trump Amurika ta kai irin wannan hari kan nmaboyar yan ta’adda tareda kashe jami’ai da dama,” in ji sabon sakataren tsaro, Pete Hegseth a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa an kai hare-haren ne a yankin “Dutsen Golis” da ke arewacin kasar ta Somalia.
Wani yanki da aka gwabza fada tsakanin dakarun Somalia da yan kungiyar Al Shebab © AFPYa kara da cewa "Wannan matakin ya kara kaskantar da ikon ISIS na tsarawa da kuma kai hare-haren ta'addanci da ke barazana ga 'yan Amurka." A farkon watan Janairu, Amurka ta fuskanci harin da ya kashe mutane 14 a New Orleans. Wanda ake zargin, tsohon sojan Amurka ne da ya tuka mota a cikin jama’a, tsohon sojan Amurka ne wanda da alama kungiyar ISIS ce ta zaburar da shi. An gano tutar kungiyar masu jihadi a cikin motarsa kuma ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar a wasu faifan bidiyo. Kungiyar IS dai ba ta da yawa a Somalia idan aka kwatanta da kungiyar al-Qaeda da ke da alaka da Shebab, amma Majalisar Dimkin Duniya ta yi gargadin a bana kan karfafa alaka da IS a kasar.
ISIS kungiya ce ta kasa da kasa da ba ta da tushe balle makama, wacce ta samo asali a yankin gabas ta tsakiya, inda ta yi nasarar kafa daular halifanci a Syria da Iraki tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019. Kungiyar, duk da haka, tana da wani mutum mai karfi a Somalia, Abdulqadir Mumin, "Shi ne mutum mafi mahimmanci, mafi iko. Shi ne wanda ke kula da hanyar sadarwa ta duniya na IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI