Amurka ta sanar da janye dukkan dakarunta da ke Somaliya.
Kakakin Rundunar Tsaron Amurka da ke Afirka (AFRICOM) Kanal Chris Karns ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, sun kwashe sojojinsu kusan 700 daga Somaliya, inda suka tura su zuwa kasashe makota irin su Kenya da Djibouti.
Da aka tambayi Karns kan ko sabon Shugaban Kasar Amurka Joe Biden zai soke hukuncin, sai ya ce bai kamata a dinga yada jita-jita ba.
Amurka ta janye sojojinta daga Somaliya a lokacin da ya rage 'yan kwanaki kadan a gudanar da zabe a kasar.