Amurka ta duƙufa wajen sasanta Haftar da gwamnatin Tripoli

Amurka ta duƙufa wajen sasanta Haftar da gwamnatin Tripoli

Wata sanarwa da Ofishin Jakadanci Amurka a Libya ya wallafa a shafinsa na X ce ke sanar da batun ganawar ta Janar Michael Langley da Khalifa Haftar a wani yanayi da Amurka ke goyon bayan ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya na daidaita tsakanin ɓangarorin da ke rikicin a Libya bayan sabuwar ɓarakar da ta kunno kai a baya-bayan nan tsakaninsu.

Ofishin jakadancin Amurkan da ke Tripoli ya bayyana cewa manyan Janarorin Sojin nata da suka kunshi Langeley da kuma Jeremy Berndt sun samu ganawa da Haftar a Benghazi da nufin samar daidaito a rikicinsa da gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar ɗinkin duniya.

Ƙarƙashin shirin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar ɗinkin duniya a Libyan ne ake ci gaba da shiga tsakani yanzu haka da nufin daidaita ɓangaren na Haftar mai jagorancin gabashin ƙasar da ke da arziƙin man fetur da kuma sauran sassan ƙasar da ke da gwamnati mai samun goyon bayan ƙasashen duniya.

Sabuwar ɓaraka ta kunno kai tsakanin ɓangarorin biyu ne tun bayan matakin gwamnatin Tripoli na korar shugaban babban bankin ƙasar wanda ya ke daga tsagin Haftar batun da ke shirin zama babban ƙalubale ga yanayi samun kuɗaɗen shigar ƙasar lura da cewa bankin ce hanya ɗaya tilo da ƙudaden cinikin mai ke shiga ƙasar wadda ta yi fama da yaƙin shekaru 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)