A cewar kungiyar mai zaman kanta, "Jami'an tsaron Congo sun tsunduma cikin wani yanayi na hauka yayin wannan kisa" ta hanyar bude wuta kan masu zanga-zangar a ranar 30 ga Agusta, 2023 a Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
"Akalla mutane 56 ne aka kashe ba bisa ka'ida ba, sannan fiye da 80 sun jikkata," in ji Amnesty.
Yawancin wadanda abin ya shafa sun kasance mabiya Yahudanci da Kiritoci.
A baya dai daya daga cikin shugaban kungiyoyin ne ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar adawa da MONUSCO ( Ofishin Jakadancin Majalisar Dinkin Duniya a DRC). Kungiyar ta ce ta gano wasu jami’an soji uku da ya kamata a yi bincike a kansu, kuma idan an samu kwararan hujjoji, za a gurfanar da su gaban kuliya kan laifukan cin zarafin bil adama.
Kungiyar ta Amnesty ta bayar da sunayen sojojin da lamarin ya shafa,da kuma suka hada da Constant Ndima Kongba, tsohon gwamnan soji na Arewacin Kivu, Kanar Mike Mikombe Kalamba, kwamandan rundunar tsaron kasar,da Manjo Peter Kabwe Ngandu, wanda ke karkashinsa a lokacin da aka kai harin.
A watan Oktoban 2023, alkalin alkalan Congo ya yanke wa Kanar Mike Mikombe da wasu sojoji uku hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari saboda "kisan kai".
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI