Rahoton da Amnesty ta fitar ya ce Sama da fararen hula 100 ne suka rasa rayukansu a gabashin jamhuriyar Congo sakamakon harbe-harben ababen fashewa a farkon watanni 6 na shekarar 2024.
Kungiyar ta zargi dukkan bangarorin biyu da ke rikici da suka hada da dakarun Congo da yan tawayen M23 da ke ikirarin kare kabilar Tutsi, sun yi amfani da manyan makamai ba bisa ka’ida ba.
Kungiyar Amnesty ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta gudanar da bincike kan wannan rikici, tare da daukar mataki kan wadannan ke da alhaki.
Tun bayan dawowar rikicin a shekarar 2021, yan tawayen M23 tare da goyon bayan sojin Rwanda kimanin dubu 4, suka kwace iko da manyan biranen gabashin Congo, lamarin da ya raba dubban mutane da muhallansu, baya ga ta’azzara bukatar ayyukan jin kai.
Duk da kokarin Angola na sasanta rikicin, hare-hare sun tsananta a kwanan nan, inda tsakanin 1 zuwa 3 ga watan Janairun 2025, aka samu munanan arangama tsakanin sojoji na Congo da wata kungiya mai dauke da makamai a Masisi da ke lardin arewacin Kivu lamarin da ya tilastawa mutane dubu 102 rasa matsugunansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI