Fitacciyar ƴar fafutukar wadda ta yi shura wajen yaɗa manufofin baiwa Mata cikakkiyar damar karatu da aiki a Tanzania baya ga kawo sauyi a tafiyar siyasar ƙasar, ƙungiyar da ta assasa ta Change Tanzania da kuma Amnesty International ne suka sanar da ɓacewarta, inda Amnesty reshen Kenya ke cewa an yi garkuwa da ƴar fafutukar ne jiya Lahadi da misalin ƙarfe 3 na yammci a yankin Kilimani na tsakiyar birnin Nairobi.
Cikin saƙon da ƙungiyarta ta wallafa a shafin X na ƴar fafutukar mai magoya baya miliyan 1 da dubu 300, Change Tanzania ta ce wasu mutane 3 ne cikin baƙaƙen kaya a wata mota ƙirar Toyota suka sace Maria Sarungi Tsehai.
A cewar ƙungiyar bisa dukkan alamu jami’an Tanzania ne suka kame ta saboda yadda ta matsawa gwamnati ƙaimi wajen ganin ta baiwa mata damarmakin rayuwa kama daga karatu da guraben aiki, baya ga samar da daidaito hatta a madafun iko, da kuma batun sauya fasalin siyasar ƙasar ciki har da samar da jajartattun shugabanni.
Garkuwa da Maria na zuwa a dai dai lokacin da ake ganin sace-sacen mutane a sassan Kenya, haka zalika a wani yanayi da Kenya ke da tarin baiwa gwamnatoci ƙasashe cikakkiyar damar kame al’ummominsu a cikin ƙasar ba tare da shiga tsakani ba, ko da kuwa hakan ya saɓawa doka.
Ko a watan Oktoban bara, Majalisar ɗinkin duniya ta yi tir da matakin mahukuntan Kenya na baiwa gwamnatin Turkiya damar yin garkuwa da wasu Turkawa 4 tare da tisa ƙeyarsu zuwa, batun da ƴan fafutuka ke cewa ya saɓawa dokokin kare haƙƙin ɗan adam.
Ka zalika ko a watan jiya Uganda ta shiga wata tattaunsawa da mahukuntan na Kenya wanda ya bata damar tisa ƙeyar jagoran ƴan adawar ƙasar Kizza Basigye wanda tuni ya fara fuskantar hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI