Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rushewar daruruwan gidaje a Sudan

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rushewar daruruwan gidaje a Sudan

Cikowar ruwan rafin Nilu da ya haifar da mabaliyar ruwa a Hartum babban birnin kasar Sudan ya yi sanadiyar rushewar daruruwan gidaje.

Sanadiyar ruwan sama da aka dinga yi kamar da bakin kwarya a yankin AL-Kelakla dake kudancin Hartum rafin Nilu yayi cikowar da bai taba yin irinsa ba a cikin karnin da ya gabata.

Hakan dai ya haifar da ambaliyar ruwan da ya yi sanadiyar rushewar daruruwan gidaje.

Shugaban kwamitin zantarwar kasar SUdan Janar Abdulfettah el-Burhan yta ziyarci yankin tare da jami'an bayar da agajin gaggawa.

El-Burhan, ya bayar da umarnin kafa sansani tare da gina gidajen wuccin gadi cikin gaggawa a yankin.

Sanadiyar ruwan sama mai tsanani da aka rinka yi a yankin tun dga ranar 1 ga watan Agusta kawo yanzu mutane 86 sun rasa rayukansu.

 


News Source:   ()