A garin Tandja na kasar Morokko, mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon afkuwar ambaliyar ruwan da ta mamaye karkashin ginin wata masana'antar tufafi.
Mahukunta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kubutar da mutane 10 daga ginin.
Ba a san adadin mutanen da ke aiki a masana'antar ba wadda aka kafa ba bisa ka'ida ba.
Ana ci gaba da aiyukan bincike kan lamarin.