Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 93 a Sudan

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 93 a  Sudan

Mutane 93 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya janyo a kasar Sudan.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Sudan ta sanar da cewa sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da yi tun ranar 1 ga Agusta zuwa yau, ambaliyar ruwa ta afku inda mutane 93 suka rasa rayukansu.

An bayyana cewar sakamakon ambaliyar ruwa, mutane 53 sun jikkata, hanyoyin ababan hawa sun lalace inda shanu sama da dubu 5 suka mutu.

Gidaje da dama a Khartoum Babban Birnin Sudan da wasu jihohin yankin sun samu matsala sakamakon ruwan sama da aka dauki kwanaki 4 a jere ana yi, wanda ya janyo cikar kogin Nil.

Hukumar Kula da Yanayi ta SUdan ta yi gargadin cewar za a ci gaba da samun ruwan sama a kasar, a sabodahaka mutanen da ke kusa da koguna da madatsun ruwa su kula sosai.


News Source:   ()