Bayanan farko da aka fitar sun bayyana mutuwar mutane 7 sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a Addis Ababa Babban Birnin Itopiya.
Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Hana Afkuwar Gobara da Kubutar da Mutane ta Addis Ababa ta fitar ta ce, mamakon ruwan saman da aka samu da yammacin Talatar nan ya janyo ambaliya.
An bayyana mutuwar mutane 7 tare da jikkatar wasu da dama sakamakon ibtila'in.
Wasu gidaje sun rushe inda ake ci gaba da aiyukan neman wadanda suka bata.