Mutane 68 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a Najeriya.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) Muhammad Muhammad ya shaida cewar, a wannan shekarar ambaliyar ruwan ta illata yankuna 320 a Abuja Babban Birnin Kasar da wasu jihohi 35.
Muhammad ya ce, mutane 68 sun mutu, wasu dubu 129 kuma sun illata.
Ya ce, ambaliyar ta janyo karancin abinci a Najeriya, gonaki da dama sun lalace inda gidaje da yawa suka rushe.
Muhammad ya kuma jaddada kudirin NEMA na ci gaba da taimakawa don inganta aiyukan jin kai a Najeriya.