Mutane 45 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama da ake yi tun watan Yuni a Jamhuriyar Nijar.
Sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Magance Annoba ta ce tun watan Yuni ake samun mamakon ruwan sama a kasar wanda ya janyo ambaliyar da ta yi ajalin mutane 45, sama da mutane dubu 226 kuma suka illatu.
Sanarwar ta ce gidaje dubu 20 da Masallatan Juma'a 24 sun kasance malale da ruwa, shanu sama da dubu 4,290 sun mutu, rumbunan hatsi 448 da sama da kadada dubu 5 da 306 na kasar nomar sun samu matsala.
Daga farkon makon nan zuwa yau gidaje da dama sun kasance a karkashin ruwa, kusan mutane miliyan 1.5 a Yamai Babban Birnin Nijar na rayuwa a kusa da kogin Nijar wanda ya cika da ruwa sosai.
A shekarar da ta gabata mutane 32 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a Nijar.