Ambaliyar ruwa ta shafi yankunan Chadi 23 bayan shafe kadadar noma dubu 432

Ambaliyar ruwa ta shafi yankunan Chadi 23 bayan shafe kadadar noma dubu 432

Mutane fiye da 550 wannan ambaliya ta hallaka yayinda ta lalata gidaje dubu 210 da kuma kashe dabbobi aƙalla dubu 72.

Baya ga zubar ruwan sama ba kakkautawa, ɓallewar koguna biyu a Chadin ya sake ta’zzara ambaliyar musamman cikin watan da muke na Oktoba inda Majalisar ɗinkin duniya ke cewa ibtila’in ya shafi mutane miliyan 1 da dubu 900 ciki har da mata masu juna biyu akalla dubu 85 da yanzu haka ke rayuwa a matsugunan wucin gadi.

Hukumar raya birane ta Majalisar ɗinkin duniya UNFPA ta ce akwai fargabar tarin cutuka a matsugunan da mutanen da ruwa ya rushe gidajensu ke rayuwa, saboda rashin tsafta da kuma sauro.

Tuni dai hukumar ta girke jami’an kiwon lafiya 248 da sanya idanu akan iyalan da ke rayuwa a sansanonin ƴan wucin gadin.

Ƙasashen yankin yammaci da tsakiyar Afrika waɗanda tun farko aka gargaɗe su game da yiwuwar fuskantar fari saboda sauyin yanayi kusan dukkaninsu sun ga zubar ruwan sama ba ƙaƙƙautawa wanda ya shafe gonaki da dama tare da lalata amfanin gona.

Miliyoyin mutane ne a ƙasashen yankunan biyu yanzu haka ke fama da matsananciyar yunwa ƙari kan bala’o’in da sauyi ko kuma ɗumamar yanayi suka haifar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)