Ambaliyar ruwa ta raba daruruwan mutane da muhallansu a Sudan

Ambaliyar ruwa ta raba daruruwan mutane da muhallansu a Sudan

Mafi yawanci iyalai na rayuwa ne a cikin makarantu don neman mafaka, bayan da yaƙi ya tilasta musu fita daga muhallan su, sai dai kuma ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka tafka a gabashin lardin Kassala ya sake jefa su cikin halin neman gurin fakewa.

Wasu faya-fayan bidiyo sun nuna yadda kayayyakin amfanin su da sutturu ke bi ta kan saman ruwa suna gudu, yayin da tantunan da suka kafa suka kakkarye.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta majalisar ɗinkin duniya ta kwatanta halin da iyalan ke ciki a matsayin matsala da ke buƙatar agajin gaggawa ba tare da wani bata lokaci ba.

Ta ce kawo yanzu an tabbatar da cewa ruwan ya raba iyalai sama da 200 da muhallansu, kuma akwai wadanda suka koma gidajen yan uwa da abokan arziki, inda suke samun mafaka.

Ƙididdiga ta nuna cewa ruwan saman ya shafi mutane sama da dubu 11 a yankin na Kassala kaɗai cikin makonni biyu da aka kwashe ana tafka ruwan saman.

Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta ce har yanzu bincikenta ya nuna cewa ruwan da za’a samu nan gaba sai ya zarce wanda aka gani a yanzu, sakamakon sauyin yanayi, iƙirarin da shugaban Ofishin hukumar bayar da agajin gaggawa na majalisar ɗinkin duniya a Sudan Bichenge Malaika Balikwisha ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)