Mutane 55 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a Ruwanda.
Labaran da jaridar New Times ta fitar na cewa gadoji 5 sun karye, gidaje 91 kuma sun kasance a karkashin ruwa sakamakon ambaliyar ruwa.
Gwamnati ta sanar da mutuwar mutane 55, kuma an fara bayar da kayan taimako ga iyalansu.
Ana sa ran ci gaba da samun mamakon ruwan saman da aka fara a watan Maris a kasar.