A Chadi wasu sabbin alkalumman da Offishin ayyukan jinkai na Majalisa Dinkin Duniya OCHA ya fitar na cewa akalla mutane sama da 500 ne suka mutu a kasar saka makon ambaliya ruwa ,yayin da wasu mutum miliyan guda da dari 7 suka tagayyara tun daga watan Yuli yi zuwa yau.
A alkalumman OCHA tace akwai gidaje sama da dubu 200 da suka ruguje yayin da ambaliyar ta lalata filayen noma sama da eka dubu 300, kazalika ruwan da aka shafe kwanaki ana shararawa sun kuma yi awongaba da dabbobi sama da dubu 69.
Tuni dai ma’aikatar ministan kula da ayyukan agaji a kasar ta sanar da kafa kwamitin da zai yi nazari kan matakan rage hadurran dake tattare da ambaliyar.
A farkon watan satumba nan , MDD ta fitar da gargadin yiyuwa samun sauka ruwan sama masu karfin gaske a yankin.
Anata bangare hukuma kula da abinci ta Majalisa Dinkin Duniya PAM, ta ce tana bukatar tallafin miliyan 16 na dala domin tallafawa kasashe 14 da lamarin ya shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI