Kusan mutane dubu 950 ne suka rasa matsugunansu a cikin wadannan kasashe uku - 649,184 a Nijar, 225,000 a Najeriya da kuma 73,778 a Mali – kamar yadda sanarwar ta nuna.
Daruruwan yara na cikin su kuma tuni suke fama da rashin lafiya da yunwa da ta samu asali saboda lalacewar amfanin gona.
Ƙungiyar ta ce ta damu da katsewar karatunsu, saboda makarantu sun zama sansanin ƴan gudun hijira, ko kuma ambaliyar ta lalata su.
Kashen da lamarin ya fi ƙamari
A Jamhuriyar Nijar, inda lamarin ya shafin sassan ƙasar, alƙaluma sun ce mutane 273 ne suka mutu yayin da ta shafi sama da mutane 700,000 tun daga farkon damina a watan Yuni a cewar gwamnati.
A makwabciyarta Najeriya, jihohi 29 daga cikin 36 na kasar, wadanda akasarinsu na arewa ne,lamarin ya shafa sakamakon tunɓasar kogunan Neja da Benue mafi girma a ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 200 ciki har da kananan yara.
A kasar Mali, inda gwamnati ta ayyana yanayi bala'in gaggawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, kusan rabin wadanda suka rasa matsugunansu yara ne, wadanda da yawa daga cikinsu na neman mafaka a makarantu, lamarin da ya haifar da tsaiko na komawarsu karatu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI