Za a dai a gudar da zaɓen ne daidai lokacin da Chadi ke samun ƙaruwar hare-haren da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da kawo ƙarshen yarjejeniyar soji tsakaninta da Faransa da ta yi musu mulkin mallaka, da kuma zargin tsoma baki a rikicin da ya dabaibaye makwabciyarta Sudan da ake yi wa Chadi.
A shekarar 2021 ne Mahamat Deby mai shekaru 40 ya karɓi jagoranci ƙasar, bayan mutuwar mahifinsa Idriss Deby Itno, wanda ya jagoranci ƙasar sama da shekaru 30.
Deby ya kuma lashe lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Mayu, inda zai kwashe wa’adin shekaru biyar kan karagar mulki, duk da cewa ƴan adawa sun bayyana sakamakon a matsayin mai cike da maguɗi
Jagoran ƴan adawar ƙasar Succes Masra da ya lashe kashi 18.5 a zaɓen shugaban ƙasar, ya ce za su kaura cewa zaɓen ƴan majalisun na ranar Lahadi, bisa zargin gwamnati da nuna son kai da danniya.
To sai dai ministan ayyuka na ƙasar Aziz Mahamat Saleh ya ce zaɓen zai bai wa shugaban ƙasar dama cimma kudurorinsa na siyasa da yake son cimma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI