Al'ummar Chadi na dakon sakamakon zaɓen ƴan majalisu da ƙananan hukumomi

Al'ummar Chadi na dakon sakamakon zaɓen ƴan majalisu da ƙananan hukumomi

A N'Djamena babban birnin ƙasar, ƴan adawa sun koka da cewa akwai kura-kurai da dama da aka a wasu yankuna, lokacin da sojoji suka kaɗa ƙuri'unsu a ranar Asabar, inda aka ga sojoji da ƴan sanda da makiyaya suna zaɓe kwana guda kafin zaɓen gama gari.

Gwamnati Chadi dai ta ce zaɓen na a matsayin mataki na ƙarshe na maida mulki kacokam kan tsarin dimukaradiya.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce kashi 52.37 na yawan waɗanda ya kamata su kaɗa kuri’a ne suka fito rumfunan zaɓen a jiya, wanda hakan ke nuna ƙarancin fitowar da aka samu.

Yadda wasu daga cikin runfunar zaɓe suka kasance a jiya. Yadda wasu daga cikin runfunar zaɓe suka kasance a jiya. AFP - JORIS BOLOMEY

Jagoran ƴan adawar ƙasar Succes Masra, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa APF cewa hakan ta faru ne sakamakon kiran da suka yi wa magoya bayansu na ƙauracewa zaɓen.

A dai shekarar 2021 ce shugaban ƙasar Mahamat Idriss Deby Itno ya hau karagar mulki, bayan rasuwar mahaifinsa wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin ƙasar, sannan ya kuma lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a watan Mayun wannan shekarar..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)