An bude runfunan zabe da misalin karfe 7 na safe agogon kasar inda za’a shafe sa’oi 10 ana kada kuri’a.
Sauyin da ake so a aiwatar ya shafi samar da shugaba mai cikakken iko da zai shafe wa’adin shekaru 7 akan kujera wanda za’a sabuntawa sau guda, sabanin wanda aka amfani da shi a kasar tsawan shekaru.
A saban kundin tsarin mulki dole ne duk wani dan kasar dake son tsayawa takara shugabancin kasar ya cika tsakanin shekaru 35 zuwa 70 a duniya.
Idan kundin ya samu amincewa zai ba shugaban kasa cikakken ikon tafiyar da majalisar zartaswasa yayin da zai nada mataimaka biyu da zasu rika dafa masa a ayyukan sa na yau da kullum.
Wasu daga cikin sauye-sauyen da kundin ya tanada sun hada da soke mukamin Firaminista abunda ke ba shugaban kasar dama sanya ido akan ayukkan ministocin gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI