Ƙalubalen da ke gaban zaɓabben shugaban ƙasar Ghana

Ƙalubalen da ke gaban zaɓabben shugaban ƙasar Ghana

A jawabinsa jiya Litinin, Mahama ya ce dole ne Ghana ta samarwa da al’ummarta wuraren zama, kulawar lafiya, abinci, tsaftataccen ruwan sha, ayyukan yi da albashi, sai dai zai fi mayar da hankali ne kan sauya fasalin tattalin arziƙin ƙasar da ke cikin wani hali.

Dramani ya ce shekaru 8 da Nana Akufo-Addo ya yi yana mulki, ya jefa tattalin arziƙin Ghana cikin mawuyacin hali, kuma shi ne babban ƙalubalen da ke gabansa, a don haka za’a ɗauki tsawon lokaci kafin magance matsalolin.

A ranar Lahadin da ta gabata ne babban abokin hamayyarsa Mahumudu Bawumia na jam’iyya mai mulki ya amince da shan kaye a zaɓen na ƙarshen mako, bayan da Mahama mai shekaru 66 ke kan gaba a samun kuri’u tun kafin sanar da sakamakon zaɓen a hukumance.

Mahama, babban ɗa ga attajirin ɗan kasuwar shinkafa kuma ɗan siyasa, ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2012 bayan mutuwar shugaba John Atta Mills wanda Mahama ya yi masa mataimaki zamanin mulkinsa.

A wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters kafin zaɓen, Mahama ya ce zai nemi a sake tattaunawa kan lamunin Dala biliyan 3 da Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya amince da bai wa ƙasar a shekarar da ta gabata domin sauya yanayin biyan basussukan da ake binta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)