Aljeriya za ta fara sarrafa allurar rigakafin Korona da hadin gwiwar China da Rasha

Aljeriya za ta fara sarrafa allurar rigakafin Korona da hadin gwiwar China da Rasha

Aljeriya ta sanar da cewa za ta fara sarrafa allurar rigakafin Korona asalin kasar China "Sinovac" da na asalin kasar Rasha "Sputnik V" kan sabon nau'in coronavirus (Kovid-19) daga watan Satumba.

Lutfi bin Bahmed, Ministan Masana'antun Magunguna na Aljeriya, ya ba da sanarwar cewa tattaunawar da ake yi da kasashen China da Rasha akan alluran rigakafin Korona na zuwa karshe.

Bin Bahmed ya ce za su fara hada magunguna guda biyu tare a watan Satumba.

A cewar sabon bayanan da Ma'aikatar Lafiya ta Aljeriya ta sanar, an samu jimillar mutane dubu 146,942 da suka kamu da cutar a kasar mai yawan mutane miliyan 45, yayin da asarar rayukan gaba daya ta kai dubu 3 da 851.

Duk da cewa Aljeriya ta sanar da yakin neman rigakafin inda za a samar da alluran rigakafi miliyan 20 ga cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin kasar, an bayyana cewa mutane miliyan 2 ne aka yiwa rigakafin a kasar kawo yanzu.


News Source:   ()