Algeria ta yi watsi da zargin lalata alaƙar diflomasiyya da Faransa ta yi mata

Algeria ta yi watsi da zargin lalata alaƙar diflomasiyya da Faransa ta yi mata

A martanin da Algeria ta yi wa Faransa ta ce ko kaɗan ba ta da hannu wurin ƙara damalmala alaƙar diflomasiyyar da ke tsakaninta da Faransa.

Ma’aikatar harkokin wajen Algeria a wata sanarwa da ta fitar, ta zargi bangaran masu tsatsatsauran ra’ayi a Faransa da yaɗa bayanai da ba na gaskiya ba kan Algeria.

Wannan cece-kuce tsakanin Faransa da Algeria na ƙaruwa a dai dai lokacin da Fransa ta mayar da wani mai fafutuka zuwa Algeria

Doulemn mai shekara 59 ya shiga hannun hukumomin Faransa a kudancin birnin Montpellier bayan ya wallafa wani bidiyo da ya janyo zazzafan cece-kuce a shafin TikTok.

An tura Doulemn zuwa Algeria ranar Alhamis kamar yadda lauyanshi ya tabbatar amma kuma an sake mayar da shi Faransa a yammacin wannan rana saboda Algeria ta ƙi karɓarshi.

Ministan harkokin wajen Fransa Jean-Noel Barrot ya yi barazanar sanya takunkumin visa ko kuma na tallafin ci gaba ga ƙasar a lokacin da yake fadawa kafar talabijin ta LCI cewa ƙasarsa ba ta da wani zaɓi face ta mayar da martani muddin Algeria ta ci gaba da ƙoƙarin lalata alaƙar diflomasiyya da ke tsakaninsu.

Sai dai Algeria ta ce dalilin da ya sa suka ƙi amincewa da ɗan fafutukar ya shiga ƙasar shine domin bashi damar kare kanshi bisa tsari da dokokin ƙasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)