A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta fitar ta bayyana cewa, Algeria ba ta cikin wata maƙarƙashiya ko bita da ƙulli da ake tunani, inda ta zargi masu rajin kare hakkin bil adama a kasar Faransa da neman aibanta ƙasar.
Hukumomin Faransa sun tsare "Doualemn", mai shekaru 59 dake ƴaɗa labarun dake tasiri a tsakanin al’uma, a kudancin birnin Montpellier bayan da ya sanya wani faifan bidiyo mai rikitarwa a shafinsa na TikTok.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka aike shi da jirgin zuwa kasar Aljeriya, kamar yadda lauyansa ya bayyana, amma an mayar da shi kasar Faransa da yammacin ranar alhamis din da Aljeriya ta ki barin mai tasiri ya shiga.
Ministan cikin gida na Faransa Bruno Retailleau a ranar Juma'a ya zargi Algeria da kokarin kaskantar da ƙasar da tai musu mulkin mallaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI