Ƙungiyar ta Alarme Phone Sahara da ke sanya idanu kan kaiwa da komon ƴan cirani tare da kai ɗauki cikin saharar don laluben waɗanda suka ɓace ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa galibin ƴan ciranin na cikin yanayin na wahala.
Ƙungiyar mai babban ofishi a birnin Yamai ta bayyana cewa Algeria ta girke waɗannan ƴan cirani cikin yanayi na wulaƙantarwa da rashin tausayi duk kuwa yadda ayarin ke ƙunshe da tarin mata da ƙananan yara.
Tun daga shekarar 2014 aka fara ganin tururuwar baƙin haure zuwa Algeria wadda ke matsayin mashiga garesu don ratsawa da nufin kama doguwar tafiya don isa nahiyar Turai ta tekun Mediterranean.
Babban jami’in yaɗa labaran ƙungiyar Moctar Dan Yaye ya shaidawa AFP cewa sun tattara alƙaluman yan ciranin da Algeria ta koro wanda yawansu ya kai dubu 19 da 798 daga watan Janairun shekarar nan zuwa Agusta.
A cewar Dan Yaye galibin ƴan ciranin kan sha baƙar wahala inda a wasu lokutan har ta kan kai ga rasa rayukansu a cikin saharar gabanin isa tuddan mun tsira, kuma da sanin hakan Algeria ke girke su a wajen.
Moctar Dan Yaye ya ci gaba da cewa jami’an tsaron Algeria kan kai sumame tare da kame baƙin haure har cikin gidajensu ko kuma wuraren ayyukansu ko ma akan iyakar ƙasar da Tunisia ta yadda ake tattara su a yankin Tamanrasset na kudancin ƙasar cikin wulaƙantaccen yanayi gabanin tisa ƙeyarsu zuwa saharar iyakar ƙasar da Nijar.
Jami’in ƙungiyar agajin ta Alarme Phos Sahara ya ci gaba da cewa ƴan ciranin waɗanda kusan dukkaninsu sun fito ne daga ƙasashen kudu da saharar afrika, na tafiyar aƙalla kilomita 15 a ƙafa, cikin sahara mai cike haɗari gabanin isa Assamaka wanda ke matsayin gari na farko akan iyakar bayan tsallake rairayin sahara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI