Algeria ta haramtawa kamfanonin Faransa shigar mata da alkama

Algeria ta haramtawa kamfanonin Faransa shigar mata da alkama

Shekaru 3 kenan ana tafka rikicin diflomasiyya tsakanin Algiers da Paris kuma ko a farkon rikicin sai da Algeria ta dakatar da kamfanonin na Faransa daga shigar mata da alkama na tsawon watanni gabanin dawo da su bakin aiki daga bisani.

Wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, wani sabin rikici ne ya kunno kai tsakanin ƙasashen biyu.

Bayanai na nuna cewa wannan dakatarwa ta baya-bayan nan ka iya ƙarfafa Rasha wadda ita ke shigar da alkama ga tarin ƙasashen gabas ta tsakiya ta hanyar amfani da tekun Black Sea.

Algeria na matsayin ƙasa mafi sayen alkamar da Faransa ke nomawa, wanda kuma shi ne wani ɓangaren na tattalin arziƙin ƙasar ta Turai, kai tsaye dakatar da hada-hadar da ke tsakaninsu zai shafi tattalin arzƙin kamfanoni da dama a ƙasar haka zalika ƙananun manoma dama tarin ma’aikata.

Ana dai ganin matakin Faransa na nuna goyon baya ga ci gaba da kasancewar yankin yammacin ƙarƙashin ikon Morocco ya fusata Algeria ƙasar da ta shafe tsawon lokaci ta na fafutukar ƴancin ƴan Polisario.

Har yanzu dai ma’aikatar kasuwancin Faransa a ƙetare ba ta yi tsokaci kan matakin na Algeria ba, wanda ta sanar tun a jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)